Tsaro

Kotu ta sake ƙin amincewa da buƙatar bada belin DCP Abba Kyari

Babbar kotu tarayya da ke Abuja wadda ke sauraren karar da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta (NDLEA) da ta shigar in da take tuhumar babban jami’in dan sanda, kuma mataimakin Kwamishinan yan yan sanda da aka dakatar a watannin baya Abba Kyari da wasu mutum shida ta ki amincewa da bukatar da lauyoyin su suka gabatar na a bayar da belin Abba Kyari.

Sai dai a zaman kotun na yau Litinin tace za ta saurari bukatar a zaman ta na gaba, in da tayi umarnin a cigaba da tsare Abba Kyari da wasu mutane biyar da aka kama su a tare.

Lauyan DCP Abba Kyari ya shaidawa manema labaran da suka yi dandazo a bakin kotun cewa kotun ta dage zaman ta zuwa ranar Litinin 14 ga watan Maris, 2022 domin sake duba batun bayar da belin Abba Kyari.

Advertisement

Amma sai dai lauyan ya ƙi cewa komai game da abubuwan da suka wakana cikin kotun har da mika wuyan da wasu mutum biyu cikin mutum shidan da ake tuhuma da aikata laifukan suka yi domin samaun salama.

Advertisement