Siyasa

Kotu Ta Kori Dan Takarar Majalisar Wakilai Na APC, Aminu Kanta

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta kori Aminu Kanta dan takarar majalisar wakilai a mazabar Babura/Garki a jihar Jigawa a zaben 2023 mai zuwa.

Mai shari’a Emeka Nwite ya kori Kanta da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jihar saboda gabatar da sunan karya.

Don haka ne kotun ta bayyana Alhaji Isa Dogonyaro a matsayin halastaccen dan takarar kujerar majalisar wakilai ta APC.

A baya dai Kanta yayi ikirarin sunan shi Ahmed Mohammed – zargin da Dogonyaro ya kalubalanta a gaban kotu, yayin da yayi zargin cewa Kanta ya tsaya zaben fidda gwani da sunan karya.

Advertisement