Tsaro

Kotu ta daure wanda ya kai kara a hukumar EFCC saboda bada bayanan karya

Mai shari’a Agatha A. Okeke na babbar kotun tarayya dake Uyo a ranar Alhamis, ta samu wani Idongesit Samuel Eyibio da laifi kuma ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Advertisement

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ce ta gurfanar da Eyibio a gaban kotu a ranar 6 ga Fabrairu, 2020, bisa laifin yaudarar hukumar ta hanyar boye muhimman bayanai ta hanyar shigar da kara kan wani lamari da wata kotun da ta dace ta yanke hukunci.

Laifin ya ci karo da tanadin sashe na 39(2)(a) na EFCC Establishment Act 2004 da kuma hukunci a karkashin sashe na 39(2)(b) na wannan dokar.

Advertisement

Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, 3 ga Maris, 2022, Mai shari’a Okeke, yace masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yiwa wanda ake tuhuma ba tare da wata shakka ba, ta yanke masa hukuncin da ya dace.

Tafiyar Eyibio zuwa gidan yari ya fara ne a shekarar 2019 a lokacin da ya rubuta takardar koke da sunan karya, yana zargin wani Aniete Ekan na Papi Events & Promotion Limited da gwamnatin jihar Akwa Ibom, ba tare da bayyana cewa akwai wani hukunci da aka yanke masa ba, a kan batun abu guda.

Advertisement