Tsaro

Kotu ta dage sauraren karar shugaban kungiyar IPOB, Kanu zuwa ranar Laraba

An dage sauraron tuhumar cin amanar kasa da ake zargin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu zuwa ranar Laraba.

Mai shari’a Binta Nyako ta bayyana hakan ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja bayan daukaka karar da tawagar masu kare shi karkashin jagorancin Mike Ozekhome ta yi.

An fara zaman kotun ne da misalin karfe 9:56 na safiyar ranar Talata inda lauyan mai shigar da kara ya roki alkalin da ya karanta tuhume-tuhume 15 da aka yi wa Kanu.

Advertisement

Sai dai kuma lauyoyin dake kare Kanu nuna adawa bisa hujjar cewa ba su da cikakken bayani game da tuhume-tuhumen da ake tuhumar shi da su, don haka zai zama rashin adalci a ci gaba da shari’ar saboda wadannan yanayi.

Sakamakon haka mai shari’a Nyako ya bayar da umarnin dage ci gaba da shari’ar a gobe.

Kafin a dage sauraron karar, Ozekhome, a wata hira da aka yi da shi a cikin kotun, ya zargi gwamnatin tarayya da rashin hannu a kan lokacin da za a fara tuhumar.

Ya kuma bayyana cewa har yanzu mambobin kungiyar lauyoyi da Kanu ba su duba tuhume-tuhumen da aka yi musu ba domin su shirya kariya.

Advertisement