Kasuwanci

Kotu Ta Bai Wa CBN Umarnin Kulle Asusun Bankin Polarish

Umarni wanda mai shari’a Adebusoye ya bayar a cikin karar da babban mai shari’a na Ondo kuma kwamishinan shari’a, Sir Charles Titiloye ya shigar ya nuna cewa wata kotun Ondo ta bayar da umarni ga babban bankin Najeriya da ya kulle asusun bankin Polaris saboda wani hukunci na bashin N2,162,561,509.84.

Advertisement

Rahotanni daga jaridar The Nation sun bayyana cewa, hukuncin da aka yanke kan karar AK/75/2017 ya bayyana cewa Titiloye ya cika bukatar ne bisa zargin gazawa da kuma rashin cika sharuddan da aka yanke na dakatar da zartar da hukuncin. An tattaro cewa bankin Polaris ya cire kudi ba bisa ka’ida ba daga asusun gwamnati da ke bankin tare da bayar da umarnin mayar da kudaden diyya.

Sai dai kuma an dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar Litinin 16 ga watan Junairu, 2023 bayan mai shari’a Adebusoye ya ba gwamnatin jihar izinin rike asusun bankin Polaris da babban bankin Najeriya.

Advertisement

Source: The Nation

Advertisement