Tsaro

Kotu ta ƙi bayar da belin Abba Kyari a shari’ar a alaƙa da kwayoyi da yake fuskanta

A ranar Litinin ne dai aka cigaba da shari’ar mataimakin kwamishinan yan sandan da aka dakatar, DCP Abba Kyari, yayin da wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta ki amincewa da bukatar lauyoyin na neman belin shi.

Advertisement

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Inyang Ekwo, yace bukatar ta biyo bayan umarnin wata kotun ta daban, inda ta baiwa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA bukatar cigaba da tsare Abba Kyari na tsawon kwanaki 14 domin ta kammala bincike.

Ya cigaba da fayyace cewa waccan kotun, wacce ta ba da umarnin goyan bayan NDLEA a ranar 22 ga Fabrairu, kotun ce mai hukumci.

Advertisement

Duk da haka, Mai shari’a Ekwo ya bayyana ra’ayin shi na sauraron karar da Abba Kyari ya shigar bayan karewar wa’adin kwanaki 14 na kotu.

Daga nan sai ya dage zaman har zuwa ranar 15 ga Maris don sauraron bukatar Abba Kyari na neman a tabbatar masa da hakkinsa.

Advertisement