Tsaro

Kisan Kebbi: Buhari ya sha alwashin magance ƴan bindiga da sauran su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bayyana bakin cikin shi kan kisan da yan bindiga suka yiwa yan banga a jihar Kebbi.

Advertisement

A ranar Litinin ne yan bindiga suka kashe yan banga 62 a wasu kauyuka biyar na karamar hukumar Sakaba/Wassagu a jihar Kebbi.

A wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar a Abuja, shugaban ya bayyana kisan da aka yiwa yan banga da ba su ji ba ba su gani ba a matsayin abin takaici, ya kuma kalubalanci jami’an tsaro da su kara kaimi tare da rubanya kokarin su domin dakile ayyukan ta’addanci da shirye-shiryen gudanar da ayyukan yan ta’addan kafin ma su kai hare-hare.

Advertisement

Yace: “Ina so in tabbatar wa yan Najeriya cewa zan yi duk abin da ya kamata don magance wannan baka’i da gaske.

“Babban abin da ya dame ni shi ne barazanar rayuwa da wadannan gungun yan bindiga masu kisa ke yi da kuma yan ta’addar da ba su da halin ko-in-kula, wadanda ko kadan ba su kula da tsarkin rayuwa.

“Yayin da nake jajanta wa iyalan wadanda wannan ta’asa ta shafa, bari na yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga jami’an tsaron mu da su kara kaimi.

“Dole ne su rubanya kokarinsu domin dakile shirin ayyukan ‘yan ta’adda kafin su kai hari.”

Advertisement