Tsaro

Kasar Rasha ta lalata jirgin sama mafi girma a duniya na Ukraine

An ba da rahoton cewa an lalata jirgin Antonov AN-225 mafi girma a duniya a lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine.

Advertisement

A cewar majiyar, an sanyawa jirgin sunan ‘Mriya’. A cikin harshen Ukrainian yana nufin ‘mafarki’.

An ce an kai harin ne a filin jirgin sama da ke wajen babban birnin Ukraine Kyiv, a rana ta hudu da mamayar Rasha.

Advertisement

Idan za a iya tunawa, sojojin Rasha sun kaddamar da harin na farko da safiyar Alhamis, duk da gargadin da Amurka da wasu kasashe suka yi.

An yi amfani da jirgin na musamman wajen jigilar kaya kuma an ce tsawonsa ya kai mita 84 (kafa 276).

Saboda haka, jirgin sama mafi girma a duniya.

Kamfanin tsaron na Ukraine wanda ke kula da jirgin ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa sake gina Mriya, zai dauki sama da dalar Amurka biliyan 3 da kuma sama da shekaru biyar.

Sai dai hukumomin Ukraine sun sanar da cewa za su sake gina jirgin dakon kaya tare da ci gaba da kare kasar.

Advertisement