Kar Ku Jawowa Najeriya Wani Yakin Basasa – Gowon Ya Gargadi Matasa

, , Comments Off on Kar Ku Jawowa Najeriya Wani Yakin Basasa – Gowon Ya Gargadi Matasa

Gowin

Tsohon Shugaban kasa kuma dattijo, Janar Yakubu Gowon ya gargadi matasa a kasar nan da ka da su jefa kasar cikin yakin basasa wanda ka iya zama sanadiyyar halaka ta.

Ya yi gargadin cewa sabon yakin basasa zai mayar da Najeriya baya a cikin mawuyacin halin da ba za a iya tsammani ba.

Janar Gowon ya yi wannan gargadin ne a ranar Asabar a Abuja a wajen taron laccar da aka shirya kan “Sauya fasalin Tsaron Najeriya.

READ ALSO:  Wani Matashi Ya Kashe Matar Sa Akan Koko (Kunu) A Jahar Neja

Tsohon shugaban kasar ya samu wakilcin tsohon gwamnan jihar Bauchi, Manjo Janar Chris Abutu Garuba.

Ya bayyana yaki a matsayin wani yanayi mara dadi sannan ya kara da cewa wadanda suka fada cikin yakin ba za su yi fatan Najeriya ta shiga wani yakin daban da wanda aka gwabza tsakanin 1967 da 1970 ba.

Gowon ya nuna matukar damuwar sa game da karuwar tashin hankali tsakanin matasa sannan ya roki gwamnatin tarayya da ta dauki mataki kan wannan kalubalen.