Kano: An Bukaci Da A Saki Mutanen Da Suka Yi Batanci Ga Manzon Allah S.A.W
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya, Amnesty International, ta bukaci a gaggauta sakin mawakin mai da’awar wakokin addinin Islama ne shi na jihar Kano, Yahaya Sheriff Aminu, wanda ake tsare da shi tun shekarar 2020 bisa zargin shi da yin batanci a cikin wasu sakonnin sauti da aka yada ta hanyar WhatsApp wanda ya zama sananne a cikin watan Maris, 2020.
Amnesty ta kuma bukaci a gaggauta sakin wani da ya bayyana kansa a matsayin wanda bai yarda da Allah ba, shi ma daga jihar Kano, Mubarak Bala, wanda aka kama shi a ranar 28 ga Afrilu, 2020, bisa rahotannin da ya wallafa a Facebook inda ake zargin shi da cin mutuncin Annabi Muhammad S.A.W.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta kuma bukaci a gaggauta sakin Ismaila Sani Isah, wanda aka kama a jihar Sokoto a watan Yulin 2021 bayan an zarge shi da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad S.A W a shafukan sada zumunta.
Da take gabatar da bukatar a kan shafinta na X, (Twitter) ranar Juma’a, kungiyar ta ce, “Amnesty International na sake kira ga hukumomin Najeriya da su saki duk wadanda ake tsare da su a gidan yari ko kuma ake shari’a bisa zargin yin sabo.
“Dole ne gwamnati ta farka cikin gaggawa kan wajibcinta na shari’a na kasa da kasa na mutunta da kare hakkin dan adam, gami da ‘yancin yin addini da bayyana ra’ayi.” Inji kungiyar.