Kasuwanci

Kananan ƴan kasuwa na cutuwa da matsalar karancin mai a Najeriya

Ilorin, Nigeria – Ga Mustapha Arinakore, rayuwa a matsayin mai tuka keken Napep mai kafa uku da yake gudanar da kasuwancin shi a birnin Ilorin da ke tsakiyar Najeriya ya dogara ne akan man fetur. Amma samun man da yake bukata don sarrafa keken nasa ya zama abu mai wahala a cikin yan makonnin nan saboda cigaba da fama da karanci a fadin kasar.

Bai iya neman alfarma daga ma’aikatan man fetur ba kuma yana da wuya ya zauna a cikin layi na sa’o’i da yawa, ya koma kasuwar bayan fage (Black Market). A can kuma lita daya na tafiya akan naira ₦500 ($1.20) maimakon naira ₦165 ($0.40) a hukumance kuma hakan yana kara matse masa yar karamar riba.

Muna siya da tsada kuma kusan ba zai yuwu a kara kudin fasinja ba saboda yawancin fasinjojin ba za su iya biya ba, ”in ji Arinakore wanda ya shaida wa Al Jazeera cewa ya samu keken sa guda uku kan siyan hayar sa saboda haka dole ne ya biya kudinsa na yau da kullun.

Advertisement

Idan ya yi sa’a ya sami gidan mai yana sayarwa, sai ya biya cin hanci da dama; na farko zuwa ga masu kula da ƙofofi sannan ga masu aikin bututun ƙarfe.

Advertisement