Kasuwanci

Kamfanonin jiragen sama a Najeriya sun dakatar da jirga-jirga akan tsadar man jirage

Kamfanonin jiragen sama na Najeriya, Airline Operators of Nigeria (AON), za su dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida daga ranar litinin saboda karin farashin man jiragen sama har ninki hudu, in ji wata kungiyar kamfanonin jiragen sama a ranar Asabar.

Ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Najeriya sun ce farashin man jiragen ya tashi daga naira ₦190 zuwa ₦700 a kowace lita daya (daga dala ($0.45 zuwa kusan dala $1.70).

An samu hauhawar farashin man jiragen sama ne saboda mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine a watan Fabrairu.

Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi a duk duniya tun lokacin da Rasha ta mamaye makwabciyarta ta yamma, wanda ya haifar da takunkumi da dama da kasashen Yamma suka kakabawa Moscow – babbar mai fitar da mai da iskar gas.

“Babu wani kamfanin jirgin sama a duniya da zai iya daukar irin wannan girgizar kwatsam daga irin wannan tashin hankalin na dan kankanin lokaci,” in ji AON, inda ya kara da cewa yanzu zai ci wa abokin ciniki kudin jirgi naira ₦120,000 ($289) na jirgin na sa’o’i daya, wanda ba shi da araha ga yan Najeriya “sun riga sun fuskanci matsaloli da yawa”.

AON, don haka, tana “akaicin sanar da jama’a cewa kamfanonin jiragen sama na membobi za su daina aiki a fadin kasar daga ranar Litinin, 9 ga Mayu, 2022, har sai an samu sanarwa,” in ji ta.

Ma’aikatar sufurin jiragen sama ta mayar da martani inda ta bukaci kamfanonin jiragen sama da su “yi la’akari da yawaitar tasirin rufe ayyukan, ga yan Najeriya da matafiya a duniya”.

Back to top button