Kamala Harris Ta Bayyana Shiga Zaɓen Shugaban Ƙasa Bayan Joe Biden Ya Fice Daga Takara
Amurka – Mataimakiyar shugabar kasa, Kamala Harris ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar shugabancin kasar.
Harris ta bayyana aniyar ta bayan Shugaba Joe Biden ya amince da ita.
Wannan na zuwa ne yayin da Biden ya miƙa wuya ga matsin lamba kuma ya fice daga takarar shugaban kasa sakamakon shekaru da matsalolin kiwon lafiya.
Duk da haka, da take mayar da martani ga amincewarta, Harris ta sha alwashin tabbatar da cewa ‘yan jam’iyyar Democrat sun lashe zaben shugaban kasa mai zuwa.
Ta kuma sha alwashin hada kan dukkan ‘yan jam’iyyar Democrat da suka ji haushi.
A cewar Harris: “Na yi farin ciki da samun amincewar Shugaban kasa kuma niyyata ita ce in samu da lashe wannan takara.
“A cikin shekarar da ta gabata, na zagaya ko’ina cikin kasar, ina tattaunawa da Amurkawa game da zabin da ya dace a wannan gagarumin zabe. Kuma abin da zan ci gaba da yi ke nan a kwanaki da makonni masu zuwa.
“Zan yi duk abin da zan iya don hada kan jam’iyyar Democrat – da kuma hada kan al’ummarmu – don kayar da Donald Trump da matsananciyar shirinsa na 2025.
“Muna da kwanaki 107 kafin ranar zabe. Tare, za mu yi yaƙi. Kuma tare za mu yi nasara.” inji Harris