Taskar Labarai

Kalli Bidiyon Yadda Aka Yankewa Yan Luwadi Hukuncin Kisa a Bauchi

Kalli Bidiyon Yadda Aka Yankewa Yan Luwadi Hukuncin Kisa a Bauchi

Babbar kotun shariar musulunci dake jihar Bauchi ta yanke wa wasu matasa biyu da dattijo hukuncin kisa ta hanyar jefewa ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022. bisa laifin yiwa wasu kananan yara luwadi.

Al’amarin ya faru ne a karamar hukumar Ningi kamar yadda jaridar BBC hausa ta rawaito.

Kotun ta samu mutanen, wanda suka hada da matasa biyu da kuma wani dattijo mai misalin sheakru 70, da wannan kazamin laifi, wanda dukkanin su suka amsa aikata lafin.

Sai dai wani ma’aikacin kotun, ya shaidawa BBC hausa cewa babu wani lauya da ya wakilci wadanan mutanen a yayin zaman shari’ar, da kotun ta yanke hukunci ranar Laraba,.

Shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar Ningi, Adamu Dan Kafi, ya fadawa wa BBC hausa cewa an kama masu laifin ne a kauyen a watan Mayu, suna amfani da kwakakwa da dabino wajen yaudarar kananan yara suna aikata luwadi da su.

Ya kuma kara da cewa masu laifin suna da damar daukaka kara cikin wata daya bayan yanke hukunci.

Back to top button