Nishaɗi

Kai-Tsaye: An Saki Dalibai Mata Na Makaranta Su 317 Da Aka Sace A Zamfara

Rahaotannin dake shigo muna sun nuna cewa an sako dalibai mata su kimanin 317 da wasu yan binidga suka sace a wata makarantar sakandire ta garin Jangebe dake cikin yankin karamar hukumar mulki ta Talatar Mafara a Jahar Zamfara, kamar yanda jaridar The Punch ta turanci ta habarta.

A halin da ake ciki yaran dukkan suna a fadar mai martaba sarkin Anka, yayin da za’ayi jigilar su zuwa babban jahar wato Gusau.

Kamar yanda jaridar The Punch ta amabata cewa wata majiya mai karfi ta tabbatar ma da jatlridar cewa an cimma matsaya tsakanin gwamnati da yan bindigar, inda har majiyar ta tabbatar ma The Punch a yau Lahadi cewa daliban zasu isa Gusau a yau.

Dalibai matan da aka sace dai a ranar Juma’ar da ta gaba ana zaton an shiga dasu dajin dake tsakanin Dangulbi da Sabon Birnin Banaga a karamar hukumar mulki ta Maru.

Back to top button