Tsaro

Kada ku kira mamayewar da aka yiwa Ukraine da ‘yaki’ – Rasha ta faɗawa kafofin watsa labarai

Yayin da hare-haren da Rasha ta kaddamar da zubar da jini a kan Ukraine ya kusan shiga mako na biyu, fadar Kremlin ta yi aiki tukuru don inganta yanayinta na al’amuran da ke cigaba da fuskantar fushi da kuma yunkurin yaki a cikin gida, wanda aka kama kusan mutane 7,000 a duk fadin kasar tun bayan barkewar rikici a ranar Alhamis.

Misali, wata sanarwa da hukumar tace fina-finai ta intanet ta Rasha, Roskomnadzor, ta yi gargadin cewa yin la’akari da yakin da ake yi na soja a matsayin “mamaye”, “kai hari” ko “bayyana yaki” zai kai ga toshe gidan yanar gizon da yayi laifi.

Abinda hakan ke nufi shine, duk wata kafar yada labaran kasar da aka samu da wallafa rikicin Ukraine da Rasha a matsayin yaƙi, hukumomi zasu rufe wannan kafar yaɗa labarai.

Advertisement
Advertisement