Tsaro

‘Kada ka koma Katsina bayan mulkin ka’, Shehu Sani ya gargadi Buhari

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada yayi ritaya bayan gama mulkin shi zuwa mahaifar shi ta Daura a jihar Katsina, saboda rashin tsaro a jihar.

Tsohon dan majalisar wanda yayi wannan gargadin a ranar Alhamis din da ta gabata ta shafinsa na Twitter, yace ya damu matuka da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a jihar da kuma yankin Arewa maso Yamma wanda yayi sanadin kashe mutane sama da 1,192 tare da sace wasu sama da 3,000, kamar yadda rahotannin da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya fitar.

A lokuta da dama dai shugaba Buhari ya sha yin tsokaci kan cewa zai yi ritaya a gonar shi ta Daura idan shekara takwas da yayi mulki za ta kare a shekara mai zuwa amma, Sani na ganin ba haka ba ne saboda matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yamma da ya cigaba da wanzuwa, tare da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kashe-kashe. fiye da kowane lokaci.

Advertisement

“Zan shawarci shugaba Buhari da kada yayi tunanin komawa Daura a karshen wa’adin mulkin shi a 2023.

‘Yan bindiga sun kashe mutane 1,192 tare da yin garkuwa da sama da dubu uku a Kaduna a shekarar da ta gabata kadai, wanda ya zarta adadin mutanen da aka kashe da kuma sace su a kasashen Yemen da Libya.

“Sace da ‘yan fashi a Katsina na kara ta’azzara a rana kuma idan jihar nan ce Shugaban kasa yana son ya yi ritaya ya zauna.

Advertisement