Siyasa

Ka roki Kwankwaso kada ya tafi, Shugaban PDP na Kano ya roƙi Saraki

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano, Shehu Sagagi, ya shawarci shugabannin jam’iyyar da su yi duk mai yiwuwa don ganin tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso bai fice daga jam’iyyar ba.

A cewar Sagagu, idan aka yi la’akari da “tsarin siyasa mai karfi na Kwankwaso,” ficewar shi daga PDP a wannan lokaci ba zai haifar da da mai ido ga jam’iyyar ba.

Sagagu yace, “Ina ba jam’iyyar PDP shawara da su tattauna da Kwankwaso, domin idan har suka bar shi ya sauya sheka, ba za ta yi wa PDP da daukacin ta dadi ba.

Advertisement

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano ya yi magana a ranar Alhamis yayin ziyarar tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na tsohon shugaban majalisar dattawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Bukola Saraki, a Kano.

Tawagar dai ta samu jagorancin Daraktan yakin neman zaben Bukola Saraki Farfesa Iyorwuese Hagber.

Advertisement