Tsaro

Juyin mulkin Guinea-Bissau: Shugaba Umaro yace an dakile mummunan yunkurin

Shugaban kasar Guinea-Bissau yace ya tsallake rijiya da baya a yunkurin juyin mulki bayan da wasu mahara dauke da bindigogi kirar AK-47 suka kai hari fadar gwamnati na tsawon sa’o’i biyar a lokacin da shugaban kasa da firaministan kasar ke ciki.

Harin da aka dakile a ranar Talata a babban birnin kasar da ke yammacin Afirka ya zo ne kimanin makonni biyu kacal bayan da sojoji suka hambarar da zababben shugaban Burkina Faso bisa tafarkin dimokuradiyya, yana mai nuna fargabar cewa wani juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan yana kara zaburar da wasu a yankin.

Shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo ya yi wa manema labarai jawabi a yammacin ranar Talata, yana mai cewa “harin dimokuradiyya” ya zo ne yayin wani taron gwamnati a ginin.

Advertisement

Embalo ya ce, “Jamhuriyar mu da jami’an tsaronmu sun yi nasarar dakile wannan aika-aika, inda ya kara da cewa an shafe sa’o’i biyar ana harbe-harbe kuma an kashe mutane ko kuma jikkata.

“Ba juyin mulki ba ne kawai. Wani yunƙuri ne na kashe shugaban ƙasa, firaminista da dukkan majalisar ministocin ƙasar,” inji shi.

Advertisement