Tsaro

Juyin Mulki: Sojoji sun ‘tsare’ shugaban kasar Burkina Faso Kabore

Wasu wasu sojoji sun tsare shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore, a cewar wasu rahotannin, kamar yadda gidan talabijin din Aljazeera ya ruwaito.

Advertisement

Rahotannin a ranar Litinin sun zo ne kwana guda bayan da sojoji suka gudanar da zanga-zanga a wasu barikokin sojoji, lamarin da ya janyo fargabar juyin mulki a kasar da ke fama da rikici. Daga baya a ranar Lahadi, an kuma ji karar harbe-harbe a kusa da gidan Kabore a babban birnin kasar, Ouagadougou.

An ga motocin sulke da dama na rundunar shugaban kasar, dauke da harsasai, a kusa da gidan da safiyar Litinin daya motar ta fantsame da jini.

Advertisement

Wasu majiyoyin tsaro biyu da wani jami’in diflomasiyyar Afirka ta Yamma sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an tsare Kabore a wani sansanin soji.

Kawo yanzu dai babu wani bayani da gwamnatin kasar ta bayar, wanda a ranar Lahadin da ta gabata ta musanta cewa ana yunkurin juyin mulki.

Advertisement