Joe Biden Ya Janye Daga Takarar Shugaban Ƙasa, Ya Goyi Bayan Kamala Harris
Shugaban Amurka Joe Biden ya karɓi kiraye-kirayen janye takararsa na sake tsayawa takara, lamarin da yasa zaben da za’a na a fadar White House na bana ya zama wani yanki mara tabbas.
Sanarwar da shugaban kasar mafi tsufa a tarihin Amurka ya yanke a ranar Lahadi, ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan jam’iyyarsa ta Democrat ke ci gaba da fuskantar matsin lamba, inda ‘yan majalisar wakilai sama da 30 suka fito fili suka yi tir da ficewar sa.
A cikin wani sako a X (Twitter), Biden, mai shekaru 81, ya ce ya zai ci gaba da zama a matsayinsa na shugaban kasa da kuma babban kwamanda har sai wa’adinsa ya kare a watan Janairun 2025 kuma zai yi jawabi ga al’ummar kasar a wannan mako.
“Ya kasance babbar daraja a rayuwata na zama shugaban ku. Kuma duk da cewa niyyata ce ta sake tsayawa takara, na yi imanin cewa zai fi dacewa ga jam’iyyata da kasata in mayar da hankali kawai kan cika aikina a matsayina na shugaban kasa na tsawon wa’adi na,” Biden ya rubuta.