Tsaro

Jirgin dakon kayan Bangladesh ya ci karo da makami mai linzami a kusa da Ukraine

Wani makami mai linzami ko bam ya afkawa wani jirgin ruwan dakon kaya mallakin kasar Bangladesh a tashar ruwan tekun Olvia na kasar Ukraine, inda ya kashe daya daga cikin ma’aikatan jirgin, kuma ana kokarin ceto sauran daga cikin jirgin, inji mamallakin jirgin na gwamnati a ranar Alhamis.

Pijush Dutta, babban darektan kamfanin zirga-zirgar jiragen ruwa na Bangladesh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “An kai wa jirgin hari kuma an kashe injiniya daya.”

“Ba a bayyana ko bam ne ko makami mai linzami ko kuma wane bangare ne ya kai harin ba. Sauran ma’aikatan jirgin 28 ba su samu rauni ba,” inji shi ba tare da bayar da karin bayani ba.

Advertisement

Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Bangladesh ya fada a ranar alhamis din da ta gabata cewa jirgin mai suna Banglar Samriddhi mai tutar Bangladesh ya makale a tashar jiragen ruwa na Olvia bayan da Rasha ta fara mamaye Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu kuma an harba makami mai linzami.

Advertisement