Tsaro
Jiragen Yakin Saman Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga A Sokoto

A ranar Litinin din da ta gabata ne wasu jiragen yakin sojoji suka kashe ‘yan bindiga a kauyen Rarah da ke karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto.
An shafe shekaru ana kai hare-hare a karamar hukumar Rabah dake gabashin Sokoto.
Yankin dai ya yi iyaka da karamar hukumar Bakura ta jihar.
A cewar dan majalisar da ke wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar Sokoto, Abdullahi Zakari, an kai harin bam da sojoji suka kai a wurare uku daban-daban, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan ‘yan bindiga.
Ya ce ‘yan fashin na dawowa ne daga haramtattun ayyukan da suke yi a lokacin da aka kashe su.