Tsaro

Jiragen Sojoji Sun Yi Ruwan Makamai A Kan Sansanin Yan Bindiga A Katsina

An kawar da yan ta’adda da dama a lokacin da jiragen yakin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) suka harba makamai masu linzami a wajen wani bikin aure da aka shirya wa daya daga cikin manyan yan bindigar jihar Katsina, in ji PRNigeria.

Daga cikin wadanda aka kashe har da Sule, fitaccen shugaban yan bindiga, wanda dan’uwa ne ga Lalbi Ginshima, kuma dan fashi “mai kisa”.

Hare-haren da dakarun sojojin saman Najeriyar suka kai a kauyen Unguwar Adam da ke karamar hukumar Dan Musa a jihar.

Advertisement

Majiyoyin leken asiri sun bayyana cewa a Katsina, a ranar Litinin din da ta gabata ne wasu sahihan bayanan sirri da sojojin sama suka samu cewa yan ta’addan sun yi hijira daga Dan Alikima zuwa Unguwar Adam domin daurin auren daya daga cikin manyan shugabannin su.

Advertisement