Labarai

Jigawa: An Kashe Mutane Biyu, Yayin Da Masu Zanga-Zanga Suka Cinnawa Sakatariyar Jam’iyar APC Wuta

An bayar da rahoton mutuwar mutane biyu yayin da wasu da dama suka samu raunuka bayan da ‘yan sanda suka harba harsashi mai rai da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga a jihar Jigawa.

Binciken da wakilin Daily Post ya samu ya nuna cewa an gudanar da zanga-zangar ne a kananan hukumomi sama da 10 da ke fadin jihar Jigawa, inda aka samu rahotannin barna tare da wawashe dukiyoyin gwamnati da na al’umma.

Rahotanni daga Dutse babban birnin jihar sun nuna cewa an harbe daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su a kofar gidan gwamnati, yayin da daya kuma aka kashe a garin Shiwarin lokacin da masu zanga-zangar suka yi yunkurin rufe hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Masu zanga-zangar sun kuma kona helkwatar jam’iyyar APC da kona motocin jam’iyyar a Dutse babban birnin jihar.

A garin Hadejia, wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa an kwantar da mutane hudu a asibiti sakamakon raunuka da kuma shakar hayaki da ‘yan sanda suka saki.

Ya kara da cewa an wawashe shagunan sayar da kayan gona a yankin.

A garin Gumel, kantin sayar kayan noma na jihar (JASCO) da gidan dan majalisar wakilai mai wakiltar Gumel, Gagarawa da Maigarati, da gidan mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar, an lalata su tare da wawashe dukiya. Masu zanga-zangar sun yi galaba akan jami’an tsaron da aka tura yankin.

Haka zalika, a Birninkudu, an jikkata mutane biyu tare da lalata wuraren ajiyar taki da hatsi da masu zanga-zangar suka yi awon gaba da su.

Haka zalika, a garuruwan Ringim, Jahun da Kazaure, masu zanga-zangar sun bazama kan tituna, suna kira da a kawo karshen rashin shugabanci nagari.

Advertisement