Siyasa

Jiga-Jigan APC 2 Da Suka Koma PDP Tun Lokacin Da Sabon Shugaban PDP Na Ƙasa Ayu Ya Fara Aiki

Daya daga cikin muhimman alkawurran da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu ya yi a lokacin da yake jawabin bude taron shine tabbatar da dawowar ‘yan jam’iyyar da suka fice daga jam’iyyar da kuma kawo shugabannin jam’iyyar APC zuwa PDP.

Kwanaki bayan rantsar da shi, jam’iyyar PDP ta fara karbar wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki. A ƙasa akwai jerin fitattun ƴan siyasa guda biyu waɗanda suka koma PDP tun lokacin da Ayu ya hau kujerar shugaban PDP na ƙasa.

Hon. John Dyegh:- Dyegh, dan siyasa a jihar Benue kwanan nan ya fice daga APC zuwa PDP tare da Dubban Magoya baya. Manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka hada da Gwamna Samuel Ortom da Dr. Iyorchia Ayu da sauran dandazon jama’a sun tarbi dan majalisar mai wakiltar mazabar Gboko/Tarka a majalisar dokokin tarayya a karo na uku a jam’iyyar PDP a wani gagarumin biki da aka gudanar a garin Gboko na jihar Benue. .

Rt. Hon. Chibudom Nwuche:– Nwuche tsohon dan majalisar tarayya ne kuma mataimakin kakakin majalisar wakilai ta hudu (1999 – 2003). Dan siyasar wanda haifaffen jihar Ribas ne wanda ya kafa jam’iyyar PDP ya bar jam’iyyar zuwa APC a 2015 jim kadan bayan nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kimanin shekaru Bakwai bayan ya koma jam’iyyar APC mai mulki, Nwuche ya koma tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP. Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ne ya tarbe shi wanda ya bayyana shi (Nwuche) a matsayin dan dimokradiyya mai kima da suna kuma zai iya karawa PDP daraja.

Advertisement