Ƙasashen Duniya 10 Da Suka Fi Kowace Ƙasa Ƙarfin Soja

Wadannan kasashe sune kasashen da ba’a tsammanin akwai wata ƙasa a duniya da ta fi su karfin sojoji idan ana maganar gwabza yaƙi, da kayan yaki a fadin duniya, wadannan kasashen sune;
1. Amurka; Kasar Amurka ita ce kasa ta daya a cikin jerin kasashen da suke da karfin soja a fadin duniya. An ƙiyasta cewa a kowacce shekara kasar tana ware kimanin dalar Amurka biliyan $601 domin harkar tsaro kawai.
Amurka na da (Sojoji na gaba a wajen yaƙi) guda 1,400,000, kuma kasar tana da Tankokin yaki guda 8,848.
An bayyana cewa Amurka na da jiragen yaki kimanin guda 13,892, sannan tana da jirgin yaki na karkashin ruwa guda 72.
2. Rasha; Karar Rasha itace kasa ta biyu cikin jerin kasashen da sukafi kowace kasa karfin soja a fadin duniya.
Rasha tana da tankokin yaki kimanin guda 15,398, kuma tana da jiragen yaqi guda 3,429.
Kasar Rasha tana da jiragen yaki na kasan ruwa guda 55, a kowacce shekara Rasha tana ware kimanin dalar Amurka biliyan $84.5 domin kula da harkar tsaro. Sannan kasar tana da (Sojojin na gaba-gaba a wajen yaƙi) guda 766,055.
3. China; Kasar china itace kasa ta 3 cikin jerin kasashen dake da karfin soja a fadin duniya, inda kasar take da tankokin yaki guda 9,150, jiragen yaki 2,860 da jiragen yaki na cikin ruwa 67.
China tana da (Sojoji na gaba-gqba) guda 2,333,000, kuma tana ware kimanin dalar Amurka biliyan $216b domin kula da harkar tsaro a kowacce shekara.
4. Japan; Kasar Japan itace ƙasa ta 4 a jerin kasashen duniya mafiya karfin soji, inda kasar take da tankokin yaki guda 678, jiragen yaki guda 1,613 da jiragen yaki na kasan ruwa 16.
Japan na da (Sojoji na gaba-gaba) guda 247,173. Haka zalika, kasar tana ware kimanin dalar Amurka biliyan $41 domin kula da harkar tsaro a kowacce shekara.
5. India; Kasar india itace kasa ta biyar da suke da karfin soji a fadin duniya, inda suke da tankokin yaki 6,464, jiragen yaki 1,905 da jiragen yaki na kasan ruwa 15.
Indiya na (Sojoji na gaba-gaba) 1,325,000. Sannan a kowacce shekara kasar tana ware kimanin dalar Amurka biliyan $50 domin kula da harkar tsaro.
6. France: Kasar faransa itace kasa ta 6 cikin jerin kasashe mafiya karfin soja a fadin duniya, inda kasar take da tankokin yaki 423, jiragen yaki 1,264 da jiragen yaki na kasan ruwa 10.
Faransa na (Sojoji na gaba-gaba) 202,761, tana kuma ware kimanin dalar Amurka biliyan $62.3 akowacce shekara domin kula da harkar tsaro.
7. South Korea; Kasar koriya ta kudu, itace kasa ta 7 cikin jerin kasashe masu karfin soji a fadin duniya, inda kasar take da tankokin yaki guda 2,381, jiragen yaki 1,412 da jiragen yaki na kasan ruwa 13.
Koriya ta Kudu tana da (Sojoji na gaba-gaba) guda 624,465. Kasar tana ware kimanin dalar Amurka biliyan $62 a kowacce shekara domin kulawa da harkar tsaro.
8. United Kingdom; Kasar Birtaniya itace kasa ta 8 cikin jerin kasashe masu karfin soji a fadin duniya, inda kasar take da tankokin yaki 407, jiragen yaki 936 da jiragen yaki na kasan ruwa 10.
Birtaniya na da (Sojoji na gaba-gaba) guda 146,980.
A kowacce shekara kasar tana ware kimanin dalar Amurka $60 domin kula da harkokin tsaron kasar.
9. Turkiyya; Kasar Turkey itace kasa ta 9 cikin jerin kasashe mafiya karfin soji a fadin duniya, inda kasar take da tankokin yaki 3,778, jiragen yaqi 1,020 da jiragen yaki na kasan ruwa 13.
Turkiyya tana (Sojoji na gaba-gaba) guda 410,500, Kasar tana ware kimanin dalar Amurka biliyan $18.2 a kowacce shekara domin kulawa da harkar tsaro.
10. Israel; Kasar Israel itace kasa ta goma cikin jerin kasashe mafiya karfin soja a fadin duniya, inda kasar take da tankokin yaki 4,170, jiragen yaki 684 da jiragen yaki na kasan ruwa 5.
Isra’ila na da *(Sojoji na gaba-gaba) guda 160,000.
A kowacce shekara kasar tana ware kimanin dalar Amurka biliyan $17 domin kulawa da harkar tsaro.
Wadannan sune jerin kasashe guda 10 a fadin duniya da sukafi kowace kasa karfin dakarun soja.