Al'umma
Jefa Bam A Wurin Bikin Mauludi A Kaduna: Magidanci Ya Rasa Ƴa’ya 13 Daga Cikin 14
A harin bam ɗin 12 ga watan Disamba, 2023 da ya hallaka fiye da mutane masu bikin Mauludi 120 a ƙauyen Tudun Biri dake gundumar Rigasa a ƙaramar hukumar Igabin jihar Kaduna, yayin da waɗansu da dama suka samu munanan raunuka, kamar yadda majiyoyi da dama suka ruwaito.
Harin bam din wanda rundunar sojin Najeriya ta kai a daren ranar Lahadin 12 ga watan Disamba, wanda tace bisa kuskure ne hakan ya faru, ta kuma nemi afuwar mazauna yankin tare da bayar da tabbacin irin haka bazata sake faruwa ba anan gaba.
Bugu da kari, harin bam ɗin ya jefa wani magidanci cikin alhini da baƙin ciki bayan da ya rasa ya’yan shi 13 daga cikin ya’yan shi 14 da yake da su, inda ɗan shi 1 kawai ya tsira daga wannan mummunan harin.
Majiya: Nagarta Radio