Nishaɗi

Jarumin Ukraine Pasha Lee ya mutu a yakin da suke yi da sojojin Rasha a Irpin

An kashe daya daga cikin fitaccen dan wasan kwaikwayo na kasar Ukraine – Pasha Lee a yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha.

Mutuwar ta shi ta faru ne a lokacin da Shell na Rasha ya afka masa yayin da aka ce sojojin Rasha sun mamaye Irpin.

Jarumi Pasha Lee yayi suna ne bayan ya yi aiki da wasu fitattun jaruman fina-finan Hollywood a lokacin shirya wasu fina-finan Hollywood da suka yi fice kamar su Lion King, Hobbit da dai sauran su.

Advertisement

Lee ya shiga cikin Rundunar Tsaron Yanki na Sojojin Ukraine don kare kasar shi daga hare-haren na baya-bayan nan na Rasha. A shafin shi na Instagram, ya bayyana hotunan shi sanye da kayan soja.

Sai dai, Sergiy Tomilenko, wanda shi ne shugaban kungiyar yan jarida ta kasar Ukraine, ya tabbatar da rasuwar Lee ta shafin shi na Facebook. “Ƙungiyar yan jarida ta ƙasa ta Ukraine ta aika ta’aziyya ga iyalin shi da kuma masoyan shi.

Shahararren dan wasan nasa dan kasar Ukraine ya yi suna a duniyar nishadantarwa bayan ya yi aiki da wasu fitattun jaruman Hollywood wajen shirya fina-finai da dama. Ya kuma yi fim a cikin fim ɗin barkwanci na 2019, ‘Meeting of Classmates’ da 2017 blockbuster movie, ‘The Fight Rules’.

Advertisement