Uncategorized

Jariri mai ido daya da aka haifa a ƙasar Yaman ya mutu bayan sa’o’i 7

An haifi wani yaro a kasar Yaman da ido daya a wani lamari da ba kasafai ba a duniya, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

Jaririn kuma yana da kwalin ido daya da jijiyar gani guda daya, wani dan jarida dan kasar Yemen Karim Zarai, wanda ya buga hotunan yaron, yace.

Haihuwar ta faru ne a wani asibiti a ranar Larabar da ta gabata a gundumar Al Bayda da ke tsakiyar kasar Yemen, a cewar shi. “Wannan lamari ne da ba kasafai aka sani ba a tatsuniyar Girika,” an ambato Zarai yana cewa.

Jaririn ya mutu bayan sa’o’i bakwai bayan haihuwar shi, kamar yadda majiyar kasar ta bayyana. Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga hukumomin lafiya a Yaman da yaki ya daidaita.

Kafafen yada labarai sun ce duniya ta ga irin wadannan abin mamaki guda shida a cikin kusan karni biyar.

Free Bonus

X