Labarai

Jaridun Najeriya: Abubuwa (7) da ya kamata ku sani a yau [29/4/2022]

Barka da safiya! Ga taƙaitattun labaran yau daga Jaridun Najeriya:

(1). Jam’iyyar APC ta mayar da martani kan satar makudan kudade da aka yi a sakatariyar ta ta kasa da ke Abuja ranar Laraba, inda ta ce kudin ba na jam’iyyar ba ne.

A jiya ne jam’iyyar ta mayar da sayar da fom daga sakatariyar ta ta kasa zuwa cibiyar taron kasa da kasa International Conference Centre (ICC) da ke Abuja.

Advertisement

(2). Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin amfani da duk wata halastacciyar hanya domin kare kuri’un ‘yan Najeriya a lokacin babban zabe na 2023. Shugaban yayi magana ne a ranar Alhamis a liyafar buda baki tare da mambobin Hukumar Diflomasiya (Diplomatic Corps).

(3). Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu na ranar ma’aikata da kuma bukukuwan Sallah na bana. Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnati a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar Dr Shuaib Belgore a ranar Alhamis.

(4). Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya roki jam’iyyar PDP da ta bashi damar kin fara zaben fidda gwaninta na shugaban kasa domin shi ne ya fi kowa burin lashe zaben jam’iyyar. Da yake jawabi ga mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar a ranar Alhamis, Atiku ya ce ya kamata a yi la’akari da shi domin ya riga ya samu kuri’u miliyan 11 a kundin sa.

(5). Shugaban jam’iyyar adawa ta People’s Democratic Party PDP na kasa Dr. Iyorchia Ayu, ya shaidawa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar cewa duk da abokai ne, ba zai yi masa aiki a matsayin dan takara ba.

(6). Gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2023, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya sayi fom na nuna sha’awa da tsayawa takara. Fom din wanda aka ce za a sayar da shi a kan Naira miliyan 100, gwamnan ya saya a ranar Alhamis a Abuja.

(7). Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ke tunanin shiga jam’iyyar All Progressives Congress domin tsayawa takarar shugaban kasa, zai fuskanci shari’a nan da kwanaki masu zuwa.

Mataimakin Shugaban/Daraktan Hulda da Jama’a na Gidauniyar Ibo Leadership Development Foundation, Dokta Law Mefor, ya ce kungiyarsa za ta garzaya kotu domin kalubalantar Jonathan idan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara.

Advertisement