Tsaro

Jamus maka wani dan kasar Gambia kan laifukan da suka hada da kisan ƴar jarida

Kasar Jamus ta tuhumi wani mutum da laifin kasancewa wani bangare na rundunar soji da ta aiwatar da kisan gilla a madadin tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh, a cewar masu shigar da kara na gwamnatin Jamus.

Wanda ake zargin, dan kasar Gambia Bai L, ana tuhumar shi da laifukan cin zarafin bil’adama, kisan kai da kuma yunkurin kisan kai, ciki har da kisan gillar da aka yiwa wata yar jaridar kamfanin dillancin labaran AFP, Deyda Hydara a shekara ta 2004.

Bai L ya yi aiki a matsayin direban tawagar da aka fi sani da Junglers tsakanin Disamba 2003 da Disamba 2006.

Advertisement

“Shugaban Gambiya na lokacin ya yi amfani da wannan sashe wajen aiwatar da umarnin kisan ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu” da nufin ” tsoratar da al’ummar Gambia da murkushe ‘yan adawa”, in ji masu gabatar da kara a birnin Karlsruhe a ranar Alhamis.

Advertisement