Laifuku

Jam’iyyar APC Ta Bai Wa EFCC Awa 72 Ta Cafke Atiku

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bukaci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta cafke dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar bisa zargin cin hanci da rashawa.

Jam’iyyar din ta kuma bayar da wa’adin sa’o’i 72 ga Hukumar EFCC, da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka masu alaka (ICPC), da kuma Hukumar da’ar Ma’aikata (CCB), da su kamo jagoran ‘yan adawar.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Festus Keyamo, a wata kara mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Janairu, ya bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su kamo tsohon mataimakin shugaban kasar bisa laifukan da suka shafi halasta kudaden haram, karya dokar da’a, hada baki, da kuma aikata laifuka. na amana da almubazzaranci.

Advertisement
Advertisement