Tsaro

Jami’an Tsaro Sun Cafke Dan Bindiga, Sun Kwato Mota, AK-47 Da Harsasai

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta cafke wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne kuma dan bindiga a Zariya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ASP Mohammad Jalige ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun kama Rilwanu Abdullahi na kauyen Damari a karamar hukumar Birnin-Gwari da bindiga kirar AK-47 dauke da harsashi 600. Ya kara da cewa an ga Abdullahi a cikin wani yanayi na tuhuma a unguwar Madachi da ke Zariya kuma da ya ga jami’an ya yi yunkurin tserewa amma sai aka bi shi aka kama shi.

Jalige ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya jagoranci jami’an bincike zuwa wani wuri inda aka samu karin wata mota kirar Volkswagen da alburusai da aka boye a cikin tankin mai da nufin gujewa jami’an tsaro.

Advertisement

Haka zalika, rundunar ‘yan sandan ta kuma tabbatar da cafke wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da daliban jami’ar Greenfield a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, CSP Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Abuja, ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin kashe biyar daga cikin wadanda aka kashe kafin a biya su kudin fansa, daga bisani kuma aka sako wasu. Ya kara da cewa wadanda ake zargin su biyun sun kuma amince cewa sun yi aiki tare da wani mai garkuwa da mutane domin yin garkuwa da wasu ‘yan sanda biyu da dan banga daya a shekarar 2021.

Adejobi ya ce jami’an su sun kuma kama wasu ‘yan ta’adda guda biyar da ake zargi da yin garkuwa da su a tsakanin Adamawa a Najeriya da Burha, Fituha da Kesu a Kamaru.

Advertisement