Laifuku

Jami’an DSS Sun Yi Dirar Mikiya A CBN, Sun Mamaye Ofishin Emefiele

Rahotannin suka shigo mana, sun bayyana cewa Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya, CBN inda suka karbe iko da ofishin gwamnan babban bankin, Mr. Godwin Emefiele, wanda ake kyautata zaton baya Najeriya.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta habarto cewa a kwai wata tashin-tashina tsakanin jami’an DSS da Emefiele busa wani babban zargi na tallafawa ta’addanci da hukumar ke yiwa gwamnan.

Idan za’a iya tunawa, hukumar ta DSS ta nemi kotu da ta bata izinin cafke Emefiele, amma ya fice daga kasar domin hutun shekara da zai kare a ranar 17 ga watan Janairu, 2023.

Advertisement

Amma watan Disamban 2022, babbar kotun birnin tarayya ta haramtawa DSS kama, gayyata, ko cafkewa ko tsare Emefiele.

Sai dai kuma a yau Litinin da jami’an DSS da suka isa hedikwatar ta CBN, sun shigo da motoci kusan 20 dauke da jami’an tsaro cikin babban shiri.

Jami’an sun kuma hana duk ma’aikatan bankin shiga ofishin Emefiele.

Haka zalika, Peter Afunanya, mai magana da yawun DSS, har bai amsa sakon neman bahasi da wakilin Daily Nigerian ya aike masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Advertisement