Iwobi Na Kusa Da Fam Miliyan 22 A Shirin Komar Shi Fulham

Dan wasan Najeriya Alex Iwobi yana daf da komawa kulob din Fulham na Landan daga Everton da ke fama da fafatawa yayin da kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa za ta kare a yau Juma’a 1 ga Satumba.
A cewar Sky Sports, Iwobi ya rigaya yana duba lafiyarsa a Fulham kafin ya koma na dindindin.
Haka kuma, Sky Sports ta bayyana cewa cinikin ya kai fam miliyan 22 wanda ya hada da add-ons.
Iwobi zai zama na baya bayan nan a kungiyar ta Fulham sakamakon sayen Raul Jimenez, Adama Traore dan wasan Najeriya Calvin Bassey, Timothy Castagne da mai tsaron gida Steven Benda.
Zai zama komawa Landan ga Iwobi bayan shekaru hudu da barinsa, wanda a baya ya kammala karatunsa a makarantar Arsenal.
Iwobi ya buga wasa da Fulham a wasan farko da Everton ta sha a Goodison Park kuma ya buga wasanni biyu kawo yanzu.
Dan wasan mai shekaru 27 ya zura kwallaye tara a wasanni 140 da ya buga wa Everton.