Tsaro

ISWAP Ta Kai Hari Sansanonin Sojoji Biyu A Borno, Sojoji Akalla 30 Sun Mutu

Mayakan kungiyar Boko Haram da ke samun goyon bayan kungiyar IS a yankin yammacin Afirka (ISWAP), wacce a baya ake kira Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, sun kai farmaki kan sansanonin soji guda biyu da ke cikin garin Malam Fatori, Jihar Borno.

Malam Fatori a karamar hukumar Abdama tana kusa da kogin Komadougou Yobe kuma yana iyaka da tafkin Chadi da Jamhuriyar Nijar.

A cewar ISWAP a cikin wata sanarwa da SaharaReporters ta gani, an kashe sojoji sama da 30 a harin da aka kai wa sojojin a ranar Asabar din da ta gabata.

Kungiyar ta’addancin ta ce mayakan ta sun mamaye wani sansanin da ke wajen garin, inda suka yi amfani da makamai daban-daban, inda suka kashe sojoji akalla 20 tare da jikkata wasu kimanin 30 na daban.

Ta kara da cewa an kona motoci biyu masu aiki yayin da aka kama wata guda.

Kungiyar ta ISWAP ta ce an cigaba da kai harin ne da yammacin ranar Asabar yayin da dakarunta suka kai hari a wani sansani na biyu a Mallam Fatori, inda suka kashe sojoji kusan 10.

Har ila yau, ta yi izgili ga wasu sojoji da ake zargin sun gudu daga sansanonin sojin.

“Harin ya auna sansanoni biyu na sojojin Najeriya a ranar Asabar a/kusa da garin Malam Fatori a Borno.

Advertisement