Tsaro

ISWAP na horar da ƴan kunar bakin wake da zasu kai hari Arewa Maso Gabas nan ba da jimawa ba – DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta bayyana cewa kungiyar yan ta’adda ta ISWAP, na horar da yan kunar bakin wake a yankin Arewa maso Gabas.

Daraktan DSS a jihar Adamawa, Babagana Bulama, yace horar da yan kunar bakin wake na da nufin kai wani mummunan hari nan ba da jimawa ba.

Bulama yace hukumar ta DSS ta samu gano aiwatar da shirin ne ta hanyar samun bayanan sirri.

Advertisement

Yayi magana ne a taron 2022 na 1st Zonal Quarterly Conference na Daraktocin Tsaro na Jihohin Arewa maso Gabas ranar Alhamis a Maiduguri, Jihar Borno.

A cewar Bulama, “Ko da yake a baya-bayan nan an rage kai hare-haren yan tada kayar baya a sassan yankin, sakamakon ayyukan yaki da ta’addanci da jami’an tsaro ke yi.

“Bayan bayanan sirri sun nuna cewa ISWAP na horar da ‘yan kunar bakin wake da nufin kai munanan hare-hare kan jami’an tsaro da kuma al’ummomi masu rauni.”

Advertisement