Labarai

Isra’ilawa Sun Mamaye Masallacin Ƙudus, An Ɗaga Tutar Isra’ila A Ciki

Rahotanni daga gidan talabijin na Aljazeera na nuni da cewa Isra’ilawa da dama sun kutsa kai cikin harabar masallacin Al-Aqsa (Ƙudus), wuri mafi tsarki na Islama, tare da daga tutar Isra’ila.

Hotunan da gidan talabijin na Aljazeera ya tabbatar ya nuna wani mutum rike da tuta yayin da dan sandan Isra’ila ke magana da shi cikin nutsuwa kuma bai yi masa rakiya da karfi ba daga harabar masallacin ba.

Lamarin ya biyo bayan kiraye-kirayen da kungiyar Beyadenu ta yi, wadda ta ce tana da nufin “karfafa alakar Yahudawa” da wuri mai tsarki, na a daga tutar Isra’ila a masallacin ranar 14 ga watan Mayu.

Falasdinawa suna daukar ranar a matsayin Nakba – ko kuma “bala’i” – wanda ya haifar da ƙirƙirar Isra’ila.

Haguwar harabar masallacin wani lamari ne da ya saba faruwa a kai a kai duk da cewa shiga wani bangare na sa haramun ne ga yahudawa saboda tsarkin wurin, kamar yadda dokar Yahudawa ta tanada.

Hukumomin Isra’ila sun kuma sha hana Falasdinawa shiga wurin domin gudanar da Sallar Juma’a tun ranar 7 ga watan Oktoba, 2023 lamarin da ya tilasta wa da dama yin sallah a kan titunan da ke kusa da tsohon birnin.

A shekarun baya ma sojojin Isra’ila sun kai hari kan Falasdinawa masu ibada a cikin masallacin.

Advertisement