Iran Ta Kaddamar Da Makamai Biyu, Yayin Da Yaki Ke Son Barkewa A Gabas Ta Tsakiya
Iran ta kaddamar da sabbin makamai da suka hada da na’urar makami mai linzami na (Arman) da aka kera a cikin gida da kuma na (Asarakhsh) na tsaron kasa da kasa.
An gudanar da bikin kaddamar da makaman guda biyu na kan motoci a gaban ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Muhammad Reza Ashtiani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IRNA cewa, tare da shigar da sabbin tsare-tsare a cikin cibiyar tsaron kasar, karfin tsaron iska (sama) na Jamhuriyar Musulunci ta Iran zai karu sosai.
Na’urar makami mai linzami na Arman “na iya fuskantar hari guda shida a nisan kilomita 120 zuwa 180 a lokaci guda”, yayin da tsarin makami mai linzami na Asarakhsh “zai iya ganowa da lalata makaman daga nisan kilomita 50 zuwa 80.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin Gabas Ta Tsakiya, inda mayakan Houthi na kasar Yemen da ke samun goyon bayan Iran ke kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke da alaka da Amurka da Birtaniya da kuma Isra’ila a tekun Bahar Maliya a wani mataki na nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza.
London da Washington sun mayar da martani ta hanyar kai hari kan mayakan Houthi a Yemen sau da yawa.