Taskar Labarai

Innalillahi Yadda Matar Aure Ta Mutu A Hatsarin Mota Yayin Kokarin Kama Budurwar Mijinta da Yake Cin Amanarta

Kwamanda Hukumar Kiyayye Haddura na Kasa, FRSC, na Jihar Cross Rivers, Maikano Hassan, ya tabbatar da cewa hatsari ya kashe wata mata mai matsakaicin shekaru a Calabar, ranar Lahadi yayin da ta ke bin ‘budurwar’ mijinta a mota.

Kwamandan wanda ya yi magana da jaridar Vanguard a daren ranar Lahadi, ya ce zura gudu fiye da kima da matar ke yi na ya janyo hadarin.

Ya ce hatsarin ya da ritsa da mota kirar Toyota Highlander da ya faru a babban titin Muritala Mohammed a Calabar ya yi sanadin mutuwar matar da ita kadai ke tuka motar.

Kalamansa:

“Duk da cewa an garzaya da mtar asibiti mafi kusa, an ce ta rasu bayan yan mintuna saboda rauni da ta samu sakamakon hatsarin.”
Vanguard ta tattaro cewa matar tana zura gudu ne tana bin mijinta wanda aka ce yana tare da wata mata da ake zargin ‘budurwarsa’ ne amma motar ya kwace mata, kuma hakan ya yi sanadin mutuwar ta.

Wata majiya wacce bata son a ambace ta ta shaidawa Vanguard cewa matar ta hangi mijinta yana fitowa dafa kantin SPAR tare da wara mace kuma ta yi kokarin tare motar mijinta da motarta kirar Toyota Highlander.

Majiyar ta ce:

“Mijinta, shi kuma ya yi kokari ya kaucewa motarta sannan ya bi babban hanya Murtala Muhammed, sannan matar ta bi shi a guje da motarta.
“A kokarin ta na cimma mijinta, motar ta kwace mata, ta kwace daga titi ta yi karo da wata bishiya, ta lalata motar ta yadda ba zai gyaru ba kuma ta kashe kanta.”

Back to top button