Kannywood
Trending

Innalillahi Wa’inna ilaihi Raji’un Yanzu Yanzu Hadiza Gabon Tace Rayuwarta Tana Cikin Hadari

Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ta faɗa wa Kotun shari’ar Musulunci da ke Kaduna cewa rayuwarta na cikin haɗari.

Daily Trust ta rahoto cewa wani Bala Musa ya kai ƙarar Jarumar ne bisa zargin ta ƙi aurensa bayan kashe mata kuɗi N396,000.

A baya Gabon ta musanta cewa bata san mutumin ba. Alƙalin Kotun ya ɗage zaman daga 28 ga watan Yuni, 2022 zuwa 1 ga watan Agusta saboda rashin lafiyar matarsa.

Da take jawabi a harabar Kotun, wacce ake zargin ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, ya ce duba da halin rashin tsaron ƙasar nan, Jarumar na jin tsoro.

A cewarsa, suna shiga damuwa kowace ranar da Kotu zata yi zaman sauraron shari’ar saboda jarumar na fama da tsegumi a wajen Kotu.

Lauyan ya ce:

“Tsaro na abun dubawa ne, tsaaron jarumar yana da amfani haka kowa da ke cikin Kotun nan har wanda ya kawo ƙarar. Rayuwata na cikin haɗari, rayuwarta na cikin haɗari, haka ta wanda ke ƙara.


“Bamu san wanda ke bibiyar shari’ar a kafafen sada zumunta ba. Nan gaba zaka iya ganin mutane da bindigu sun zo nan sace mutane, wannan shi ne abun da ya dame mu ba wai shari’ar ba.”

Lauyan ya roƙi Kotu ta duba tsaron wacce yake wa aiki ta amince a cigaba da shari’ar ba tare da tana halarta ba.

Innalillahi Wa'inna ilaihi Raji'un Yanzu Yanzu Hadiza Gabon Tace Rayuwarta Tana Cikin Hadari

Bangaren masu ƙara ba su yarda ba
Da yake martani, Lauyan mai ƙara, Barista Naira Murtala, ya yi watsi da uzurin Gabon na rashin zuwanta zaman Kotu, inda ya ce dole wacce ake ƙara ta halarci zama.

Game da tsaron mai ƙara da wanda ake ƙara, Ya ce ba zai yi musu kan buƙatar ba saboda ƙasar ba tsaro, amma yana buƙatar yin nazari a kai.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Khadi Rilwanu Kyaudai ya tabbatar musu da cewa Kotu zata duba tsaron kowane ɓangare a zama na gaba.

Back to top button