Taskar Labarai
Trending

Innalillahi Wa’inna ilaihi Raji’un Yan Bindiga Sun Sace Amarya da Ango Ana Tsaka da Shagalin Biki a Katsina

Ƴan Bindiga Sun Shigo Garin Katsina Sun Sace Ma’aurata, Sun Harbi ‘Yan Sintiri

A Daren Jiya Ƴan Bindiga Suka Kai Hari A Unguwar Shola Dake Bayan Asibitin Koyarwa Ta Gwamnatin Tarayya, Cikin Garin Katsina, Inda Suka Sace Mata Da Mijinta, Matashi Yusuf Bishir Da Matarsa.

Haka zalika yan bindigan sun harbe wasu yan sintiri biyu dake aikin bayar da tsaro a Unguwar inda suka kashe daya daga cikin su yayin da dayan kuma yana asibiti yana karbar kulawar likitoci.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da yan bindigar suka kai hari a ƙauyen dake bayan barikin Sojoji na garin Katsina suka sace mutane suka tafi da su.

Haka zalika duk a cikin satin da ya gabata yan bindigar sun kai hari a ƙauyen Dan Tsauni dake a hanyar Babbar Ruga bisa Titin Batsari suka kashe Mutane suka kore Dabbobi tare da tafiya da wasu Mutanen.

Back to top button