Taskar Labarai

Innalillahi Wa’inna ilaihi Raji’un Mayakan IPOB Sun Fille Kan Yan Nijar 8 a jihar Imo

Rahotanni daga jihar Imo a Tarayyar Najeriya na cewa al’ummar Hausawa na cike da fargaba yanzu haka biyo bayan wani farmakin ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan IPOB wadanda suka fille kawunan wasu ‘yan Nijar 8 tare da yin awon gaba da kawunan.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Imo da ke tabbatar da harin, ta ce a litinin din makon nan ne mayakan na IPOB suka kai hari kauyen Orogwe na garin Owerri da ke dauke da galibin Hausawa ‘yan Najeriya da Nijar da ke ci rani tare da kisan mutanen.

Yayin farmakin gomman mutane sun jikkata yayinda mayakan suka fille kawunan mutum 8 dukkaninsu ‘yan Nijar tare da yin awon gaba da kan amma suka bar gangar jikin.

Jaridar Najeriya ta Daily Trust ta ruwaito wani ganau na cewa maharan sun yi tsammanin dukkanin wadanda ke cikin ginin da suka kaiwa farmakin Hausawa ne ‘yan arewacin Najeriya dalilin da ya sanya yin kan mai uwa da wabi.

Wasu Hausa da jaridar ta zanta da su a yankin sun bayyana yadda s uke rayuwa cikin fargaba saboda hare-hare ba kakkautawa da IPOB ke kai musu garin a kowacce rana tare da kashewa ko kuma jikkata mutane.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Imo ta tabbatar da afkuwar harin sai da bata bayar da tabbacin adadin mutanen da aka kashe ba, haka zalika ba ta fayyace ko maharin sun tafi da kawunan mutanen da aka kashe ko akasin haka ba.

Back to top button