Ingantaccen Maganin Olsa Na Gargajiya Mai Sauƙin Haɗi

A yau zamu yi muku bayani game da wani maganin Olsa mai inganci wanda wani bawan Allah ya roki da a sanar da dukkan yan uwa domin taimako fi sabilillah.

Kamar yadda kowa ya sani ciwon Olsa ba sai mun wani dogon bayani akan shi ba. Saboda masu fama da irin wannan lalurar sun san komai game da shi.

Yanzu zamu yi bayani ne kawai game shi wannan maganin na gargajiya wanda da yardar Allah idan aka yi yanda zamu bayyana, za’a samu waraka.

Abu na farko da za’a yi shine a samu Ayaba kuma wacce ake kira (Plaintain), wato babar Ayaban nan kuma wacce take zanwa shar, wato bata nuna ba, kamar guda 3 ko 4 zuwa 6.

Za’a ɓare Ayabar sai yan-yanka ta guntu-guntu sannan a samun Gallon mai cin lita 4 sai a zuba a cikin shi, daga nan a cika shi da ruwa.

Idan an cika Gallon ɗin sai a rufe sosai kuma a ajiye shi har tsawon kwanaki 3, bayan waɗannan kwanakin sun ciki, za’a fara fara shan wannan maganin kofi 2 da safe awa 2 kafin a ci wani abinci.

Idan kuma an gama cin abincin safen sai a kara shan kofi 1.

Haka ma da dare ko rana za’a dinga yi har wannan Gallon ɗin ya kare.

Za’a yi irin wannan hadin har sau 3, wato Gallon 3 za’a yi.

Inshaa Allah, da yardar Ubangiji an gama da wannan matsalar rashin lafiya na Olsa, wato gyalbon ciki (Ulcers).

Tunatarwa: Lokacin da za’a fara bude Gallon za’a ga yana wani tuƙuƙi, to kada a damu wannan ba komai ne ba.

Mun gode, kuma a turawa yan uwa domin wasu amfana.