Tsaro

Indiya ta harba makami mai linzami bisa kuskure cikin yankin Pakistan

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Indiya ta amince cewa ta harba makami mai linzami bisa kuskure zuwa cikin makwabciyar ta Pakistan.

A baya dai kwararrun sojoji sun yi gargadin hatsari tsakanin makwabtan wadanda suka gwabza yake-yake uku tare da yin fadan soji da dama.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar tsaron kasar ta ce an harba makamin ne bisa kuskure zuwa cikin makwabciyar ta sakamakon wata matsala da ta samu a lokacin atisayen kula da makamin.

Advertisement

Sanarwar ta kara da cewa: “A ranar 9 ga Maris, 2022, a cigaba da gudanar da aikin gyara na yau da kullum, wata matsala ta fasaha ta kai ga harba makami mai linzami cikin bazata.

“An samu labarin cewa makamin ya fado ne a wani yanki na Pakistan. Duk da cewa lamarin abin takaici ne matuka, amma kuma abin akwai sauki yadda ba a samu asarar rai ba sakamakon kuskuren ba.”

“An kuma gayyaci jami’in hulda da jama’a na Indiya a Islamabad, babban birnin Pakistan, zuwa ofishin harkokin waje don wata gagarumar zanga-zanga.”

Ma’aikatar ta ce gwamnati ta bayar da umarnin gudanar da wani babban bincike kan lamarin.

Advertisement