Al'umma

Indiya: Haramcin sanya Hijabi ga dalibai mata tauye yancin addini ne – Amurka

Indiya – Ambasada US-AT-LARGE mai kula da yancin addini ta kasa da kasa (IRF) Rashad Hussain a ranar Juma’a yace “Kada jihar Karnataka ta tantance halaccin sanya tufafin addini” da kuma hana sanya hijabi a makarantu suna cikin cin zarafin yancin addini da kuma kyamatar mata da yan mata.

Advertisement

Wannan ya zo ne a ranar Juma’a lokacin da ministan harkokin wajen kasar S Jaishankar ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a Melbourne, inda shugabannin biyu suka yi nazari kan kokarin karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, da kuma ta hanyar kungiyar Quad a yankin tekun Indiya mai ma’ana.

Hussain, wanda ya taba rike mukamin jakadan Amurka na musamman a lokacin mulkin shugaba Barack Obama a kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC), kwanan nan gwamnatin Biden ta nada shi a matsayin wakilin Amurka kan yancin addini na kasa da kasa.

Advertisement

Idan dai za’a iya tunawa, jihar Karnataka dake ƙasar Indiya ta haramta sanya a hijabi a makarantun yankin, lamarin da ya har zuka Musulmai har ya kai zanga-zanga da rufe makarantu.

Advertisement