Tsaro

Imo: Ƴan Bindiga Sun Tarwatsa Ofishin Ƴan Sanda Da Bam, Suka Saki Mutanen Da Ake Tsare Da Su

A ranar Alhamis ne wasu yan bindiga suka kai harin bam a hedikwatar yan sandan karamar hukumar Ideato ta Kudu da ke Dikenafai a jihar Imo.

Sun sako mutanen da aka tsare. Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Maharan wadanda suka zo da yawa sun banka wa wani bangare na ofishin yan sandan wuta da bama-bamai.

Bama-baman sun lalata ofishin gudanarwa, ofishin jami’an yan sanda na shiyya, da kuma ofishin karbar baki.

Shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Ideato ta kudu Fasto Bede Ikeaka ya bayyana kaduwarsa da faruwar lamarin.

Kakakin rundunar yan sandan Imo, Michael Abattam, babban Sufeton ‘yan sandan, yace har yanzu ba a yi masa bayani ba. Yayi alkawarin komawa ga manema labarai idan ya tattara bayanai.

An kuma samu labarin cewa wasu yan banga na yankin sun kama wasu daga cikin wadanda ake tsare da su da suke kokarin tserewa.

Advertisement