Al'umma

Illela: Mutanen Da Fulani Ƴan Ta’adda Suka Kashe A Munwadata, Kalmalo Da Rumji Ya Kai 20

Hoto: wani bafulatani dake yan sandar jihar Ogun suka kama dauke da bindiga kirar AK-47

Rahotanni dake shigo muna daga majiyoyi na musamman a halin da ake ciki daga wasu garuruwan dake yammacin ƙaramar hukumar mulkin Illela dake jihar Sakkwato sun nuna cewa adadin mutanen da Fulani ƴan ta’adda suka kashe daga daren jiya Lahadi zuwa yau Litinin ya kai 20.

Kamar yanda rahotanni suka bayyana, jiya Lahadi da dare yan bindigar sun kustsa cukin garin Munwadata misalin karfe 3 saura wasu yan mintuna inda suka sace wasu mata sannan suka bindige mutum 7 a daren.

Mutanen yankin da sauran makwabta da suka suka harzuƙa game da lamarin sun bi yan yan bindigar zuwa cikin dajin da bai da nisa da garuruwan da abin faru lamarin da yayi ƙarin sanadiyyar mutuwar mutane akall 13 kawo yanzu.

Tun a daren jiya Fulani ƴan ta’addar ke harbin mutane ba ƙaƙƙautawa kafin daga bisani a hangi fitulu da danjojin baburan yan bindigar a cikin daji inda suka yi awon gaba da aƙalla mutane 2, kuma ana hasashen mata ne.

Kamar yanda majiyoyin suka tabbatar a garin Munwadata an kashe mutane 7, Kalmalo 10 da Rumji mutane 3.

Karin bayani na nan tafe….

Back to top button