Tsaro

Illela: Mutane 12 sun mutu a harin da ƴan bindiga suka kai wa ƴan bindigar da suka tuba

Wasu yan bindiga a ranar Juma’a sun kashe akalla mutane 12 a wani hari da suka kai wa tubabbun yan bindiga a kauyen Illela da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Mazauna yankin sun tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin.

Ƴan bindigan, a cewar mazauna kauyen, sun afkawa kauyen ne akan babura da dama da sanyin safiyar Juma’a inda suka far wa tubabbun yan bindigar da wani Mani Turwa ya jagoranta, suna gadin al’umma.

Advertisement

Sai dai tawagar Turwa ta kore su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya yi shiru kan adadin wadanda harin ya rutsa da su.

Ya kara da cewa an tura jami’an tsaro na hadin gwiwa zuwa kauyen domin wanzar da zaman lafiya.

Advertisement